30 Oktoba 2025 - 13:17
Source: Almanar
Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Yi Maganin Duk Wani Kutsen Isra'ila A Yankunan Ƙasar

A ganawarsa da Kwamandan Sojojin Lebanon Janar Rudolph Haykal a Fadar Baabda a safiyar Alhamis, Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umurci sojojin da su fuskanci duk wani kutsen Isra'ila a yankunan kudancin da aka 'yanto, don kare kasar Lebanon da kuma tsaron 'yan kasarta.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Janar Haykal ya yi wa Shugaban kasa bayani game da bayanan kutsen Isra'ila da ya faru a sanyin safiyar yau Alhamis a garin Blida, da kuma shahadar ma'aikacin hukumar Ibrahim Salamah yayin da yake gudanar da aikinsa.

Shugaba Aoun ya bayyana cewa "wannan harin, wanda ya kasance cikin jerin ayyukan Isra'ila masu tsauri, ya zo ne jim kadan bayan taron Kwamitin Kula da Yarjejeniyar Dakatar da ayyukan ta'addanci, wanda ake sa ran ba wai kawai zata takaita rubutu ba ne, har ma za tai aiki don kawo karshensu ta hanyar matsa wa Isra'ila lamba da kuma tilasta mata ta bin sharuddan yarjejeniyar watan Nuwamba da ya gabata da kuma dakatar da take hakkin yancin ƙasar Lebanon".

A wani ɓangaren kuma, Janar Haykal ya yi wa Shugaba Aoun bayani game da ci gaban binciken kisan matashi Elio Abu Hanna da waɗansu masu ɗauke da makamai suka yi a sansanin 'yan gudun hijira na Shatila, musamman bayan miƙa wuyan mutane shida da ake zargi da hannu a harbin.

Shugaba Aoun ya jaddada "wajibi ne a ci gaba da binciken don gano gaskiyar abin da ya faru, yayin da a lokaci guda kuma ake ƙara himmar jami'an tsaro don hana bayyanar makamai da kuma bin diddigin waɗanda suka aikata laifin da kuma waɗanda ke da hannu a ciki".

Your Comment

You are replying to: .
captcha